Philippians 4

1Saboda haka, kaunatattu ‘yan’uwana da nake marmari, farin ciki na da rawani na, a wannan hanya ku tsaya daram cikin Ubangiji, kaunatattun abokai. 2Ina rokon Afodiya, ina rokon Sintiki, ku zama da ra’ayi daya cikin Ubangiji. 3Babu shakka, ina sake rokon ku, abokan tarayyar takunkumina na gaske: ku taimaka wa matayen nan. Domin mun yi wahala tare a cikin yada bishara tare da Kilimas da sauran abokan aiki na, wanda sunayensu na rubuce cikin littafin rai.

4Yi farin ciki cikin Ubangiji kullayomi. Ina sake cewa, yi farin ciki. 5Bari dukan mutane su ga jimirin ku. Ubangiji ya yi kusa. 6Kada ku damu da kowanne abu, maimakon haka, cikin komai tare da addu’a, da rokeroke, da godiya, bari rokeroken ku su sanu ga Allah. 7Salamar Allah, da ta zarce dukan ganewa za ta tsare zuciyarku da tunaninku cikin Almasihu Yesu.

8A karshe, ‘yan’uwa, duk abin da ke mai gaskiya, duk abin da ya isa ban girma, duk abin da ke mai adalci, duk abin da ke mai tsabta, duk abin da ke karbabbe, duk abin da ke kawo kauna, duk abin da ke da kyakkyawan ambato, idan akwai yabo, yi tunani a kan wadannan abubuwan. 9Wadannan abubuwan da kuka koya kuka karba kuka ji kuka gani a rayuwa ta, ku aikata wadannan abubuwan. Allah mai salama zai kasance tare da ku.

10Na yi farin ciki sosai cikin Ubangiji domin yanzu a karshe kun sabunta kulawar ku game da ni. Kun kula da ni da gaske kwanakin baya, amma ba ku samu zarafin taimako ba. 11Ba don bukata ta bane nake fada wannan. Domin na koyi dangana a kowanne irin yanayi. 12Na san yadda zan zauna cikin bukata, na kuma san yadda zan samu a yalwace. A kowace hanya cikin kowanne abu na koyi asirin yadda zan ci da yawa da yadda zan zauna da yunwa, yadda zan zama a yalwace kuma in zama cikin bukata. 13Zan iya yin komai ta wurinsa shi da yake karfafa ni.

14Duk da haka, kun yi zumunta da ni cikin kunci na. 15Kun kuma sani, ku Filibiyawa, cewa da farkon bishara, lokacin da na bar Makidoniya, babu ikilisiya da ta tallafe ni cikin batun bayarwa da karba sai ku kadai. 16Ko lokacin da nake Tassalonika, kun aika da gudumawar biyan bukatu na fiye da sau daya. 17Ba domin ina neman kyauta ba ne. A maimakon haka, ina neman amfani da zai kawo karuwa cikin ajiyar ku.

18Na karbi dukan abubuwan, ina da shi a yalwace. An kosar da ni. Na karba ta hanun Abafroditus abubuwa daga wurinku. Shesheki na dadin kamshi mai dandanno, karbabbiyar hadaya mai gamsarwa ga Allah. 19Allah na zai cika dukan bukatunku bisa ga yalwarsa da ke cikin daukaka cikin Almasihu Yesu. 20Yanzu bari daukaka ta tabbata ga Allah da Ubanmu har abada abadin. Amin.

21Gai da kowanne mai bi cikin Almasihu Yesu. Dukan ‘yan’uwa da ke tare da ni suna gaisuwa. 22Dukan masu bi a nan suna gaisuwa, musamman wadanda suke gidan Kaisar. 23Bari alherin Ubangijin Yesu Almasihu ya zauna tare da ruhunku. Amin

Copyright information for HauULB